• Ana Ci Gaba Kiran Da A Jinkirta Sanar Da Sakamakon Zaben Shugaban Liberiya

A daidai lokacin da ake jiran hukumar zaben kasar Liberiya ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Talatar da ta gabata, babban jam'iyyar siyasa ta kasar ta bukaci da a jinkirta sanar da sakamakon zaben.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar jam'iyyar "The Liberty Party" wanda dan takaranta Charles Brumskine na daga cikin wadanda ake ganin za su lashe zaben ta bukaci hukumar zaben kasar Liberiyan (NEC) da ta jinkirta sanar da sakamakon sabon abin da ta kira tabka magudi da ba daidai ba yayin zaben, yana mai cewa matukar hukumar zaben ba ta yi haka ba, to kuwa za ta garzaya kotu.

Rahotanni dai sun ce tsohon tauraron kwallon kafa na duniya dan kasar wato George Weah da mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai su ke suke kan gaba gaba a zaben kuma guda daga cikinsu ne ake ganin zai lashe zaben da maye gurbin Madam Ellen Sirleaf Johnson wacce ta shafe kimanin shekaru 12 tana mulkin kasar.

A bisa tsarin mulkin kasar dai idan ba’a samu dan takarar da ya samu kashi 50% na kuri’un da aka kada din ba, to za a je aje zagaye na biyu na zaben wanda za a gudanar a ranar 7 ga watan Nuwamba mai kamawa.

 

Tags

Oct 12, 2017 17:24 UTC
Ra'ayi