• Nijeriya : Mutum 35 Suka Mutu A Sabon Rikicin Filato

Rahotanni daga Nijeriya na cewa mutane a kalla 35 ne suka gamu da ajalinsu a sabon rikicin da ya barke a wasu kauyuka dake jihar Filato a tsakiyar kasar.

Jagororin wakilan kauyukan sun shaida wa masu aiko da rahotanni cewa mutum 29 ciki har da mata da yara ne suka mutu a yayin da dama suka jikkata a rikicin safiyar jiya Litini.

Sauran guda shida an kashe su ne a wani hari ranar Lahadi da ta gabata, a yayin da aka kone gidaje da dama.

'Yan sandan jihar Filato sun tabbatar da aukuwar rikicin da yammcin jiya, sai dai ba tare da bayyana alkaluman mutanen da rikicn ya rutsa da su ba.

Hukumomin jihar Filato dai sun jibge wani adadi mai yawa na jami'an tsaro a yankin da aka ayyana dokar hana fitar dare sanadin rikicin kwanakin baya.

 

Tags

Oct 17, 2017 05:51 UTC
Ra'ayi