• Kungiyar Hizbullah Ta Lebanon Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta'addancin  Somaliya

Tashar telbijin din almanar ta Lebanon ta ambato bayanin na kungiyar Hizbullah da a ciki ta yi tir da harin da 'yan ta'adda suka kai a birnin Magadishu.

Kungiyar ta Hizbullah ta bayyana harin da cewa laifi ne mai girma da masu makauniyar zuciya suka kai.

A ranar asabar din da ta shude ne, aka kai harin ta'addanci a birnin Magadishu na Somaliya wanda ya ci rayuka da jikkata fiye da mutane 500.

Bayanin na kungiyar Hizbullah ya kuma ce; 'Yan ta'addar suna son amfani da addini ne domin bai wa manyan kasashen duniya damar cimma manufofinsu.

Ministan watsa labarun kasar Somaliya Abdurrahman Umarm Usman, ya sanar da cewa adadin wadana suka mutu sun kai 276, sai kuma 300 da suka jikkata.

Oct 17, 2017 12:34 UTC
Ra'ayi