Oct 19, 2017 06:23 UTC

Kwararrun sun fito ne daga kasashen mambobi na kungiyar tarayyar Afirka domin tattauna matsalolin da suka shafi batun 'yan gudun hijira.

Wani batun da mahalarta taron suka maida hankali wajen tattaunawa, shine tsaro akan iyakokin kasashensu, bisa la'akari da cewa hakan wata dama ce ta bunkasar tattalin arziki a cikin nahiyar.

Mahalarta taron sun kuma tattauna batun yin Zirga-zirgar mutanen nahiyar a tsakanin kasashe wanda ba shi da sauki a yanzu, alhali 'yan kasashen waje suna kai da komowa ba tare da wata wahala ba.

A ranakun juma'a da asabar masu zuwa ne  manistocin kasashen wajen na Afirka za su dauki matakan da suka dace akan batutuwan da aka bijiro da su a taron na kigali.

Tags

Ra'ayi