Nov 18, 2017 11:20 UTC
  • Girgizar Kasar Iran : Shugaban Najeriya Ya Aike Da Sakon Ta'aziyya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya jajanta wa shugaban Iran, Hassan Rauhani da al'ummar kasar, game da dimbin asarar rayuka da girgizar kasar da ta aukawa kasar ta haifar a ranar Lahadi data gabata.

Wata sanarwa da Kakakinsa Garba Shehu ya fitar, ta bayyana girgizar kasa da aka yi a yammacin lardin Kermanshah na Iran a matsayin mai ciwo matuka.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma mika irin wannan jaje ga gwamnati da al'ummar Iraki bisa asarar dukiya da rayuka da suka yi sanadiyyar girgizar kasar da ta auku akan iyakar kasar da Iran.

Tags

Ra'ayi