Dec 01, 2017 05:50 UTC
  • Bayanin Karshen Taron Koli Na Kungiyar AU Da Turai

An kammala taron koli na kungiyar tarayya Afrika da Turai karo na biyar a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast inda shugabanni nahiyoyin biyu suka kudirin anniyar yaki da kwararar bakin haure ba bisa ka'ida ba, da kuma kalubalen dake cikinsa kamar cinikin bakin haure a Libiya.

Bangarorin sun sha alwashin kai Ayyukan agaji cikin gaggawa a Libiya, da kuma ganin bayan cibiyoyin masu safara da kuma gudanar da bincike na kasa da kasa kamar yadda shugaba kasar Ivory Coast data karbi bakuncin taron, Alassane Ouattara, ya sanar a yayin jawabin rufe taron.

Takwaransa na Guinea, kana shugaban kungiyar tarayya Afrika, Alpha Conde, ya bukaci kwamitin kare hakkin bil adama na kungiyar ta AU da ya jagoranci binciken. 

Sannan kuma ya bukaci a kafa rundina ta musamen kan masu safara bil adama.

A cewar shugaban kwamitin kungiyar ta AU, Musa Faki Mahamat, bakin haure 3,800 ake bukatar kwashewa cikin gaggawa daga kasar ta Libiya.

An dai cimma wadannan matakan ne a yayin wani taron gaggawa kan batun a daura da taron, wanda ya hada kasashen Faransa, Chadi, Nijar, MDD, da AU da EU.

Shugaba Emanuel Macron na Faransa ya tabo batun kwashe 'yan Afrika dake bukatar ficewa daga Libiya cikin gaggawa, da kuma kafa rundina ta musamen da zata kunshi 'yan sanda da jami'an leken asiri, da kuma wani gangami na sadarwa don fadakar da matasa akan yawan taburada.

Mayan matakan da shuwagabannin nahiyoyin biyu suka dauka don kawo karshen irin wannan hijira ba bisa bisa ka'ida ba sun hada da :

►bayar da ilimi da kuma horo 

shugabannin Afrika da na Turai din sun cimma matsaya ta kara zaga dantse a cikin vikin birane da karkara don samar da ilimi na gari musamen ga diya mata.

►Kwanciyar hankali da Tsaro 

Abu na biyu da bangarorin suka sa a gaba shi ne : daukar matakai kan shinfida zaman lafiya, tabbatar da tsaro da mulki na gari, da kuma taimakawa hanyoyin yaki da ta'addanci, ciki har da goyan baya da kuma taimakwa rundinar hadin gwiwa ta kasashen G5 Sahel, wacce har yanzu ta ke bukatar tallafi.

►Zuba jari 

Abu na uku shi ne hada tallafi da zuba jari don karfafa tattalin arziki ta yadda zai isa ga mafi yawan jama'a.

►Kwararar bakin haure

Abu na karshe da taron karo na biyar ya maida hankali a kai shi ne daukar matakan dakile masu safara bakin haure, da kuma duba hanyoyin shiga turai ra sawake kuma bisa ka'ida ga masu kananan ayyuka da daliban jami'a da kuma masu neman karin ilimi.

Babban abunda ya sanya taron na AU da turai na wannan karo ya fi maida hankali kan batun bakin haure, shi ne faifan bidiyo da kafofin yada labarai suka yi ta wallafawa a baya bayan nan wanda ya nuna yadda ake cikinin bakin haure tamakar baki a kasar Libiya.

Taron ya samu halartar shugabanni kasashe dana gwamnatoci kimanin 80 da kuma wakilai 5,000.

Sama da 'yan Afrika miliyan 700 dai na da shekaru 25, kuma kashi 60% na al'ummarta matasa ne.

Dayewa daga cikin matasan kuma suna barin kasashen su ne don neman tafiya turai saboda matsalar rashin aiki, talauci da kuma rashin gata ko makoma mai kyawo a kasashensu.

Tags

Ra'ayi