• Sarkin Moroko Ya Yi Gargadi AKan Hatsarin Mayar Da Ofishin Jakadancin Amurka Zuwa Kudus

A jiya talata ne sarki Muhammad Sadisu ya aike wa da shugaban kasar Amurka sako yana mai cewa; Da akwai matukar damuwa a cikin shirin mayar da ofishin jakdancin Amurka zuwa birnin Kudus

Sarkin na kasar Moroko wanda shi ne shugaban kwamitin kula da birnin Kudus a karkashin kungiyar kasashen musulmi, ya ci gaba da cewa; Birnin na Kudus yana da muhimmanci a wurin dukkanin saukakkun addinai uku, ba a wurin musulmi kadai ba.

Sarikin na kasar Moroko ya ci gaba da cewa da akwai kudurorin Majalisar Dinkin Duniya wadanda suke kira da  a nesanci samar da duk wani sauyi dangane da yanayi na siyasa da birnin na kudu yake ciki.

Kasashen musulmi da kungiyoyi da dama sun yi gargadi akan sakamakon da zai biyo bayan  matakin da Amurka take son dauka na mayar da ofishin jakadancinta daga Telaviv zuwa Kudus.

Tags

Dec 06, 2017 06:30 UTC
Ra'ayi