• An Sauya Kwamandan Sojin Da Ke Yaki Da Boko Haram A Nijeriya

Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da sauya kwamandan shirin nan na fada da kungiyar Boko Haram na Operation Lafiya Dole Manjo Janar Attahiru Ibrahim sakamakon ci gaba da munanan hare-hare da kungiyar take yi cikin 'yan kwanakin nan.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar wani kakakin rundunar sojin ta Nijeriya ne ya shaida masa hakan inda ya ce tuni aka nada Manjo Janar Rogers Nicholas a matsayin wanda zai maye gurbinsa a wannan matsayi.

A watan Mayun wannan shekarar ta 2017 ne dai aka nada Manjo Janar Attahiru Ibrahim din a matsayin kwamandan Operation Lafiya Dole din da ke fada da 'yan ta'addan kungiyar ta Boko Haram  bayan da aka sauya wa tsohon kwamandan Manjo Janar Lucky Irabor wajen aiki.

Cikin 'yan watannin baya-bayan nan dai kungiyar ta Boko Haram ta kara kaimi wajen kai hare-hare ta hanyar amfani da mata da kananan yara lamarin da ke kara sanya gwamnatin Muhammadu Buhari ta Nijeriya din cikin mawuyacin hali bisa la'akari da alkawarin da ta yi na tabbatar da tsaro musamman a yankunan Arewa maso Gabashin Nijeriyan inda 'yan Boko Haram din suka fi kai hare-haren.

A baya ma dai babban hafsan sojin kasa na Nijeriya Manjo Janar Tukur Buratai ya taba ba wa Janar Ibrahim din wa'adin kwanaki 40 da ya kamo shugaban kungiyar Boko Haram din Abubakar Shekau da kuma kawo karshen hare-haren kungiyar to sai dai kuma hakan ba ta samu ba.

 

Tags

Dec 07, 2017 05:54 UTC
Ra'ayi