• Hukumar Kula Da Farashin Man Fetur A Nigeria Ta Ce Babu Wani Shirin Kara Farashin Mai

Hukumar kayyade faracin man fetur a Nigeria ta ce gwamnatin tarayyar bata da wani shiri na kara farashin man fetur a sabuwar shekara

Jaridar daily Trust ta nakalto shugaban hukumar Abdulkadir Saidu yana fadar haka a jiya Laraba, ya kuma kara da cewa kamfannin NNPC ta kasa ita ce babbar kamfani mai samar da man fetur a kasar don haka babu wata fargaba ta samun karancin man fetur ko kuma kara farashinsa a shekara mai zuwa.

Shugaban hukumar ta PPPRA ya bayyana haka ne don sake dawowar layuka a gidajen mai a duk fadin kasar don fargaban da mutane suke yi na cewa za'a sami karancin man ko kuma akwai yiyuwan gwamnati ta kara farashinsa.

 

Dec 07, 2017 10:22 UTC
Ra'ayi