• Uganda Ta Dauki Matakan Tsaro Masu Tsanani Kan Sansanin Yan gudun Hijirar Sudan Ta Kudu A kasarta

Jami'an tsaron a kasar Uganda sun dauki matakan tsaro masu tsanani kan sansanin yan gudun hijira kasar Sudan ta kudu da ke kasar don hana daukarsu cikin rundunonin yan tawayen kasar.

Kamfanin dillancin labaran Xinhuwa na kasar China ya nakalto majiyar sojojin kasar ta Uganda tana fada a jiya Laraba kan cewa sun dauki matakan tsaro masu tsanani kan sansanin yan gudun hijira Sudan ta Kudu da ke kasar don hana yan tawayen kasar karkashin jagorancin Riek Masha daukar yan gudun hijirar a matsayin sojoji.

Labarin ya kara da cewa a halin yanzu akwai yan gudun hijirar sudan ta kudu kimani miliyon guda a kasar uganda.  Tun cikin watan Decemban shekara ta 2013 ne gwamnatin kasar Sudan ta Kudu take fafatawa da yan tawaye karkashin jagorancin Riek Macha wanda yake tsare a kasar afrika ta kudu a halin yanzu.

Tags

Dec 07, 2017 11:46 UTC
Ra'ayi