• An Yanke Hukuncin Kisa Kan Wasu 'Yan Ta'adda 13 A Masar

Kotun kasar Masar ta yanke hukuncin kisa kan wasu mutane 13 da ta same su da laifin aikata ta'addanci a kasar

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya habarta cewa a wannan Alkhamis babbar kotu ta jihar Al-Jiza ta kasar Masar ta yankin hukuncin kisa kan wasu mutane 13 sannan kuma ta yankin hukuncin daurin rai da rai ga wasu 17 na daban bayan da ta same su da laifin alakar da kungiyoyin 'yan ta'adda da kuma halartar wasu hare-haren ta'addanci da aka kai cikin kasar

Baya ga hakan, kotun ta yankewa wasu mutane biyu  hukunci daurin shekaru 15 da kuma shekaru 5 ga wasu mutane 7 na daban a gidan yari.

Rahoton ya ce wadanda aka hukuntar manbobin kungiyar ta'addancin nan ne  ta Ajnad, wacce ta kaddamar da hare-haren ta'addanci cikin kasar a shekarar 2016, kafin hakan dai dakarun tsaron na Masar sun hallaka shugaban kungiyar mai suna Hamam Muhamad.

A cikin shekarun baya-bayan nan kasar ta Masar na fuskantar hare-haren ta'addanci, mafi muni daga cikinsu shi ne wanda aka kwanaki 13 da suka gabata a babban masallaci Al-arish na yankin arewacin Sinai wanda ya yi sanadiyar ajalin mutane sama da 300.

Tags

Dec 07, 2017 18:59 UTC
Ra'ayi