Dec 07, 2017 19:00 UTC
  • Kungiyar Tarayyar Afirka Za Ta Kwashe Bakin Haure Dubu 20 Daga Libiya

Kungiyar tarayyar Afirka ta dauki kudirin mayar da bakin haure dubu 20 zuwa kasashen su daga kasar Libiya.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto kungiyar tarayyar Afirka cikin wani jawabi da ta fitar a daren jiya laraba ta ce babban abinda yake gabanta a halin yanzu mayar da 'yan kasashen Afirka dubu 20 da aka gano su kuma ake tsare da su a wuraren da suka daban-daban kuma suka nuna sha'awarsu na komawa kasashensu cikin makunni shiga masu zuwa.

Kafin hakan dai kungiyar ta AU ta sanar da cewa kafin karshen wannan shekara wato cikin makunni uku masu zuwa za ta kwashe bakin haure na kasashen Afirka dubu 15 dake jibke a kasar ta Libiya, sannan ta ce duk wata hidima da ya kamata a yiwa bakin hauren da kuma kwashe su daga cikin kasar suna kan kananen ofishin jakadancin Afirka dake birnin Tripoli.

Kungiyar AU ta ishara da cewa tuni wasu kasashen Afirka sun fara kwashe 'yan kasar su daga kasar ta Libiya, faifan vidion da aka watsa game da yadda ake cinikayar 'yan kasashen Afirka a matsayin bayi a Libiyan ya tayar da hankulan al'ummar duniya , musaman ma 'yan kasashen Afirka

Tags

Ra'ayi