Dec 12, 2017 06:26 UTC
  • Mutane Biyu Ne Suka Mutu Sanadiyar Tashin Bom A Cikin Masallaci A Kamaru

Akalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu sanadiyyar tashin bom a cikin masallaci a garin Kerawa da ke kan iyaka da tarayyar Nigeria a arewacin Kamaru.

Kamfanin dillancin labaran AFP daga Yawunde ya bayar da rahoton cewa, lamarin ya auku ne bayan sallar asubahi a jiya Litinin, lokacin da jama'a sun ragu a cikin masallacin sai wani dan kunan bakin wake ya tarwatsa kansa sannan ya kashe mutane biyu.

Jami'an tsaro a yankin sun tabbatar da wannan labarin sun kuma bayyana cewa wannan irin aikin kungiyar yan ta'adda ta Boko haram ne. 

Tun lokacin da kasar Kamaru ta fara yaki da mayakan wannan kungiyar a shekara ta 2014 ya zuwa yanzu mutane kimani 2000 ne suka rasa rayukansu tsakanin fararen hula da kuma jami'an tsaro. Mafi yawan hare-haren kungiyar na aukuwa ne a yankin arewacin kasar ta Kamaru.

Tags

Ra'ayi