• An Kama Wasu Masu Zanga-Zangar Yin Allah Wadai Da Amurka A Kasar Masar

Wani babban lauya a kasar Masar ya bada sanarwan cewa jami'an tsaro a birnin Al-Kahira sun kama wasu daga cikin wadanda suka gudanar da zanga-zangar yin Allahwadai da shugaban kasar Amurka kan abin da ya shafi birnin Qudus.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya nakalto Barrister Khalid Ali yana fadar haka a jiya Litinin, ya kuma kara da cewa masu zanga-zanga 8 ne jami'an tsaron kasar suka tsare a ranar Asabar da ta gabata a birnin Al-Kahira.  Barrister Ali ya ce ana tuhumar masu zanga-zangar 'ya'yan kungiyar Ikhwanul Muslimin ne.

Gwamnatin shugaba Abdulfatah Sisi dai ta haramta kungiyar ikhwanul-Muslimin a kasar bayan juyin mulkin da ya yi wa Mohammad Mursi a shekara ta 2013. 

A ranar Laraba 6 ga watan Disamaban da muke ciki ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bada sanarwan amincewarsa da birnin Qudus a matsayin babban birin Haramtacciyar Kasar Isra'ila, duk da cewa shugabannin kasashen duniya da dama da kuma manya manyan kungiyoyin kasa da kasa sun nuna adawarsu da daukar wannan matakin.  

Tags

Dec 12, 2017 06:27 UTC
Ra'ayi