Dec 14, 2017 12:23 UTC
  •  Boko Haram Ta Kai Hari Kan Sansanin Sojin Nijeriya A Jihar Borno

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kaddamar da wani hari kan sojojin Nigeriya a Kauyen Mainok da ke karamar hukumar Kaga a jihar Borno da ke shiyar arewa maso gabashin kasar da nufin kwace iko da barikin soji.

Rahotonni da suke fitowa daga Nigeriya suna bayyana cewa: Wasu gungun 'yan kungiyar Boko Haram sun yi dirar mikiya kan sansanin sojin Nigeriya da ke kauyen Mainok a karamar hukumar Kaga da ke jihar Borno a jiya Laraba da nufin kwace iko da sansanin lamarin da ya haifa da gumurzu tsakanin bangarorin biyu tare da hasarar rayuka.

Wasu rahotonni sun bayyana cewa: Gumurzun tsakanin bangarorin biyu ya lashe rayukan 'yan kungiyar Boko Haram 14 tare da tarwatsa motocin yakinsu biyu.

Kauyen Mainok dai yana nisan kilomita 58 ne da garin Maiduguri fadar mulkin jihar Borno da ke shiyar arewa maso gabashin Nigeriya.

 

Tags

Ra'ayi