Dec 25, 2017 17:12 UTC
  • Kasar Ghana Ta Kare Kuri'ar Kin Amincewa Da Matsayar Trump Kan Kudus Da Kasa Ta Kada A MDD

Kasar Ghana ta bayyana cewar ka kada kuri'ar rashin amincewa da matsayar Amurka na bayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila a yayin zaman babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ne don tabbatar da matsayar kungiyar Tarayyar Afirka da kuma kuma kudururrukan Majalisar Dinkin Duniyan.

Jakadiyar kasar Ghana ta dindindin a Majalisar Dinkin Duniyar, Martha Amama Pobee, ta bayyana hakan cikin wani sako da ta watsa a shafinta na Twitter yayin da take amsa tambayar wani da ya bukaci hakan inda ta ce kuri'ar da kasar Ghana ta kada din yayi daidai ne da tsohuwar matsayarta kan rikicin Palastinawa da Isra'ilawa da kuma kudururrukan da MDD da kungiyar Tarayyar Afirka suka fitar kan wannan lamarin.

Jakadiyar ta kara da cewa matsayar da Amurka ta dauka kan Kudus din wani karen tsaye ne ga kokarin kafa kasashe biyu da kuma matsayar da aka dauka tun da jimawa na cewa ta hanyar tattaunawa ce kawai za a iya tabbatar da matsayar Kudus din.

Haramtacciyar kasar Isra'ilan dai, ta hanyar ofishin jakadancinta da ke kasar Ghana ta bayyana damuwarta dangane da wannan matsaya da kasar Ghana ta dauka kan wannan kudurin, sai dai kuma kasar Ghana ta nuna ba ta yi dan da na sani kan hakan ba.

Kasar Ghana dai tana da cikin kasashe 128 da suka kada kuri'ar kin amincewa da matsayar da Amurkan ta dauka kan Kudus din a kuri'ar da aka kada a babban zauren a kwanakin baya.

 

Tags

Ra'ayi