Jan 03, 2018 07:12 UTC
  • Zanga-Zangar Nuna Kiyayya Ga Gwamnatin Togo Tana Ci Gaba Da Yin Kamari A Kasar

Zanga -zangar nuna kiyayya ga gwamnatin Togo tana ci gaba da gudana a kasar, inda ake ci gaba da samun dubban daruruwan mutane suna gudanar da zanga-zanga a birnin Lome fadar mulkin kasar.

Zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin Togo da gamayyar jam'iyyun siyasar adawar kasar suka kira tana ci gaba da gudana a sassa daban daban na kasar musamman birnin Lome fadar mulkin kasar ta Togo, inda masu zanga-zangar suke ci gaba da jaddada yin kira ga shugaban kasar Faure Gnassingbé kan ya yi murabus daga kan mukaminsa.

Tun a watan Satumban shekarar da ta gabata ta 2017 ne gamayyar jam'iyyun adawar kasar Togo da suka kai jam'iyyu 14 suka bukaci al'ummar kasar da a duk sati su fito zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin Faure Gnassingbe da nufin matsa masa lamba kan ya yi murabus daga kan karagar shugabancin kasar tare da jaddada bukatar gudanar da gyarar fuska a kundin tsarin mulkin kasar ta hanyar sanya ayar doka da zata takaita wa'adin tsayawa takarar shugabancin kasar zuwa wa'adin shugabanci sau biyu kacal.

Kasar Togo dai ita ce kasa daya tilo a yankin yammacin Afrika da bata da takamammen wa'adin tsayawa takarar shugabancin kasa lamarin da ya bai wa zuriyar Gnassingbe damar gudanar da shugabancin kasar ta Togo har na tsawon rabin karni. Sakamakon haka a wannan sabon boren siyasa da ya kunno kai a kasar Togo ke neman aiwatar da gyara a kundin tsarin mulkin kasar da nufin kawo karshen mulkin zuriyar Gnassingbé. Har ila yau 'yan adawa a kasar Togo suna zargin cewa: Kane-kane da zuriyar Gnassingbé suka yi a harkokin mulkin Togo ya hana gudanar da tsabtaceccen tsarin dimokaradiyya a kasar lamarin da duk zaben da aka gudanar a kasar zuriyar Gnassingbé ke lashewa.

Bayan bullar zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a kasar ta Togo a watan Nuwamban shekarar da ta gabata; shugaban kasar Faure Gnassingbé ya bayyana amincewarsa da bukatar 'yan adawar kasar ta neman gudanar da gyare-gyare a kundin tsarin mulkin kasar, amma abin da yaki amincewa da shi a cikin jerin bukatun nasu shi ne bukatar yin murabus daga kan karagar shugabancin kasar kafin karshen wa'adin mulkinsa da kuma batun kayyade wa'adin tsayawa takarar shugabancin kasar zuwa wa'adi biyu kacal.

A fili yake cewa: Ci gaba da habakar dambaruwar siyasa a kasar Togo tsakanin gwamnatin kasar da 'yan adawa tana bukatar tsoma bakin kasashen da suke makobtaka da kasar da ma kungiyar hadin kan kasashen yankin da nufin warware rikicin kasar ta hanyar lumana, kamar yadda matakin gudanar da garambawul a kundin tsarin mulkin kasar ta Togo da nufin shimfida tsarin dimokaradiyya mai inganci ita ce hanya daya tilo da zata haifar da zaman lafiya da sulhu a kasar.

 

 

Ra'ayi