• Sojojin Nigeria sun Kubutar Da Mutane Kimani 700 Daga Hannunn Boko Haram

Mutane kimanin 700 ne sojojin Nigeria suka kubutar daga hannun boko haram da suke yin garkuwa da su.

Kamfanin dillancin labaran Farsnews ya nakalto daga tashar talabijin ta Aljazeera cewa, kakakin sojojin Nigeria Colonel Timothy Antigha ne ya bayyana hakan, ya kuma kara da cewa mafi yawan mutanen mata ne da yara masu kamun kifi da manoma daga yankin tabkin chadi. 

Labarin ya kara da cewa mayakan na boko haram sun tilastawa mutanen yankin tabkin chadi zama a wasu tsibirai a cikin Tabkin na lokaci mai tsawo. 

Kakakin sojojin ya kara da cewa sun gano wadannan muatane ne a kusa da garin Monguno daga gabacin jihar Borno.

 

Tags

Jan 03, 2018 11:47 UTC
Ra'ayi