• Sudan Ta Nuna Damuwarta Da Matsayin Masar Kan Tattaunawar Madatsar Ruwan Annahdah

Gwamnatin kasar Sudan ta yi wasti da bukatar ware ta daga tattaunawar madatsar ruwa ta Annahdah ta kasar Ethiopia wanda kasar masar ta so a yi.

Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar Iran ya nakalto Saifuddeen Ham shugaban bangaren gyare-gyare na ma'aikatar ruwa a kasar Sudan yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa duk da cewa har yanzun gwamnatin kasar Ethiopia bata aiko mata da wannan matsayin a hukumance, amma jaridun kasar sun bayyana cewa shugaban kasar Masar Abdul Fatah Sisi ya bukaci gwamnatin kasar Ethiopia ta fidda kasar Sudan cikin shirin tattaunawa kan madatsar ruwan. Ta kuma maida shi tsakanin kasashen biyu da kuma Bankin Duniya kawai. 

Madatsar ruwa ta Annahdah wacce ake kan ginawa a kan kogin Nilu a cikin kasar Ethiopia ita ce madatsar ruwa mafi girma a nahiyar Afrika, kuma idan an kammala ta zata haddasa fari da karancin ruwa a kasar ta Masar.

Tags

Jan 03, 2018 11:54 UTC
Ra'ayi