• Gwamnatin Algeria Ta Kara Matsawa Wajen Yaki Da Fasa-kwabrin Makamai A Kan Iyakokin Kasar

Jami'an tsaron kan iyaka na kasar Algeria sun kara tsananta yaki da fasa-kwabrin makamai zuwa cikin kasar daga kan iyakokin kasar.

Shafin yanar gizo na Al-Arabia Aljadid ya bayyana cewa kafin wannan sanarwar jami'an tsaron kasar sun gano wasu rumbunan makamai a wasu yankun hamada da kuma kan iyakokin kasar wadanda yan ta'adda suke tarawa.

Labarin ya kara da cewa jami'an tsaron sun gano cewa yan ta'adda suna da shirin yin amfani da wadannan makamai wajen kawo babban tashin hankali a kasar. Sannan a kwai yiyuwar su dauki wadannan makamai zuwa wasu kasashen yammacin Afrika wadanda suke ta fama da yan ta'adda. 

Wata majiyar ta sojojin kasar ta Algeria ta bada labarin gano wani rumbun ajiye makamai a garin  Burj-Boji Mukhtar na kan iyaka da kasar Mali, ta kuma kara da cewa dukkan makamai an shigo da su kasar ne ta kan iyakarta da kasar Libya wacce take fama da yan ta'adda.

Tags

Jan 03, 2018 11:55 UTC
Ra'ayi