• Gwamnatin Equatorial Guinea Ta Sanar Da Rusa Wani Yunkurin Juyin Mulki A Kasar

Ma'aikatar tsaron kasar Equatorial Guinea ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun yi nasarar rusa wani yunkurin juyin mulki da sojojin haya suka shirya gudanarwa a kasar.

A bayanin da ministan tsaron kasar Equatorial Guinea Nicolas Obama Nchama ya fitar a yau Laraba yana dauke da cewa: Jami'an tsaron kasar sun yi nasarar rusa wani yunkurin juyin mulki da wasu sojojin haya da suke samun tallafi daga wajen kasar suka shirya a cikin watan Disamban shekarar da ta gabata.

Nicolas Obama ya kara da cewa: Jami'an tsaron Equatorial Guinea sun samu nasarar rusa yunkurin juyin mulkin ne da taimakon jami'an tsaron kasar Kamaru, kuma sojojin hayar sun samu horon soji ne daga 'yan tawayen kasar ta Equatorial Guinea.

Tun a ranar 27 ga watan Disamban da ya gabata ne sojojin gwamnatin Kamaru suka sanar da kame wasu gungun 'yan bindiga a kan iyakar kasarsu da Equatorial Guinea, inda 'yan bindigar suke kokarin kutsawa cikin kasar ta Equatorial Guinea. 

Jan 03, 2018 19:32 UTC
Ra'ayi