• Sojoji Masu Bore A Ivory Coast Sun Kai Hari Da Kona Wani Barikin Soji

Rahotanni daga kasar Ivory Coast sun bayyana cewar wasu sojoji masu bore a garin Bouake, gari na biyu mafi girma a kasar, sun kai hari kan wani barikin zaratan sojojin kasar da ake kira da CCDO a garin a daren jiya inda suka kwashi makamai da kuma sanya wuta a wasu bangarori na barikin

Su dai wadannan sojojin, wadanda a shekarar da ta gabata ma sun taba yin irin wannan boren, suna zargi zaratan sojojin ne dai da yi musu leken asiri da tattaro bayanan sirri a kansu.

Rahotanni sun ce tun a ranar Talatar da ta gabata ce dai aka fara wannan boren bayan karar bindigogi da harbe-harbe da manyan bindigogi da aka yi a birnin bayan da rikici da gumurzu ya barke tsakanin bangarori biyun.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo wani kakakin gwamnatin kasar na tabbatar da faruwar rikici da harbe-harben sai dai ya ce babu wani da ya rasa ransa, yana mai cewa tuni aka tura da karin sojoji garin don tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

A bara ma dai an sami irin wannan bore na sojin daga garin na Bouke wanda daga baya ya bazu zuwa wasu garuruwa na kasar.

 

Tags

Jan 11, 2018 05:48 UTC
Ra'ayi