Jan 11, 2018 19:03 UTC
  • 'Yan Kungiyar Boko Haram Sun Kai Hare-Hare Kan Yankunan Arewacin Kasar Kamaru

Majiyar tsaron Kamaru ta sanar da cewa: Wani gungun 'yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kai hare-hare kan yankunan da suke arewacin kasar, inda suka kashe mutane uku.

A sanarwar da majiyar tsaron kasar Kamaru ta fitar a yau Alhamis yana dauke da cewa: Wani gungun 'yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kaddamar da harin wuce gona da iri kan al'ummar yankin Kolofata da ke arewacin kasar Kamaru a cikin daren jiya Laraba, inda suka kashe mutane akalla uku.

Har ila yau a cikin daren na jiya mayakan kungiyar ta Boko Haram sun kai hare-hare kan kauyuka da dama da suke kusa da garin Mayo Moskota da ke makobtaka da kasar Nigeriya lamarin da ya tilastawa al'ummun kauyukan tserewa daga muhallinsu.

Wani basarake a yankin Kolofata ya bayyana cewa: Mayakan kungiyar Boko Haram sun kaddamar da hare-haren a cikin daren jiya ne kan yankunan garin da nufin neman abinci domin rahotonni suna nuni da cewa: Kayayyakin Abinci sun kare a sansanonin mayakan kungiyar don haka suke fantsa garuruwa domin sace kayayyakin abincin jama'a.  

 

Tags

Ra'ayi