Jan 12, 2018 06:34 UTC
  • A Tunisia Ana Tsare Mutane Fiye Da 600 Sanadiyyar Tashe-Tashen Hankula Na Baya -Bayan nan

Ma'aikatar cikin gida na kasar Tunisia ta bayyana cewa tana tsare da mutane kimani 600 sanadiyar zanga-zangar kin gwamnatin kasar.

Shafin yanar giza na labarai mai suna Dovan ya nakalto ma'aikatar ta cikin gida tana fadar haka a jiya Alhamis, ta kuma kara da a ranar Laraban da ta gabata jami'an tsaron kasar sun kama mutane 328 tare da zargin sata, daukar ganimar kayakin jama'a, koma gine-ginen gwamnati da kuma toshe manya-manyan tituna.

Ma'aikatar ta kara da cewa a ranakun Litinin da Talaba kuma sun kama mutane 280 daga cikin wadanda suke zanga zangar nuna kiyayya ga gwamnatin kasar sanadiyyar mummunan matsalolin tattalin arzikin da kasar ta fada ciki.

An fara zanga-zangar nuna damuwa da matsin rayuwan da ake ciki a kasar ta Tunisia ne a ranakun farko na wannan shekara ta 2018 bayan da gwamnatin kasar ta bada sanarwan dakatar da tallafin da take yiwa wasu kayayyakin abinci wanda ya kai da tashin farashin kayakin nan take.  

Tags

Ra'ayi