• Sudan Tana Sanya Idanu Akan Kai Da Komowar Sojojin Masar Da Eritrea

Mataimakin Shugaban Kasar Sudan Ibrahim Mahmud ne ya sanar da haka yana mai bayyana kai da komowar sojojin makwabtan nasu biyu a matsayin barazana ta tsaro ga Sudan.

Mataimakin shugaban kasar ta Sudan ya bayyana haka ne dai kwanaki kadan bayan da kasarsa ta aike da sojoji da tankokin yaki zuwa jahohin Kasala da Sava da suke iyaka da Masar da Eritrea.

Alakar Sudan da Masar ta yi kamari akan tsibirin Halayeb da Sudan take zargin Masar da mamaye shi.  sai kuma batun gina madatsar ruwa a kasar Habasha, da Masar take dauka a amtsayin barazana ga ruwawan maliyan da yake kwarara zuwa cikinta, yayin da Sudan take daukar shi a matsayin mai amfani a gare ya.

Tags

Jan 12, 2018 11:56 UTC
Ra'ayi