• Kungiyar Tarayyar Afirka Ta Yi Kakkausar Suka Kan Cin Mutuncin Da Shugaba Trump Ya Yiwa Nahiyar Afirka

Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi kakkausar suka kan cin mutuncin da shugaban kasar Amurka Donal Trump ya yi wa al'ummar Nahiyar Afirka.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Ebba Kalondo kakakin Shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afirka Moussa Faki na cewa kungiyar A U na alawadai da fircin shugaban kasar Amurka na cin mutuncin 'yan kasar Afirka da ya yi a jiya Alkhamis.

Ebba Kalondo ya kara da cewa Shugaban na Amurka ya ci zarafin al'ummar kasar Afirka da ma 'yan asalin kasashen Afirkan da aka kai Amurka a matsayin bayi, kuma cikin karni na 21 abin kunya ne ga Amurka da shugaban ta zai firta irin wadannan kalamai

Kalaman wulakancin da Mr Trump ya yi sun faru ne a lokacin da 'yan majalisar daga jam'iyyun kasar suka kai masa ziyara ranar Alhamis domin gabatar masa da kudirin dokar shige-da-fice wanda suka amince da shi.

Tags

Jan 12, 2018 19:08 UTC
Ra'ayi