• 'Yan Tawaye Sun kai Hari A Gabashin Congo

'Yan tawaye sun kai hari a garin Beni dake jahar Kivo Ta Arewa a gabashin jamhoriyar Demokaradiyar Congo

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto wata majiya a jamhoriyar Demokaradiyar Congo na cewa kimanin mutane 10 ne ciki har da wani dan jarida aka yi awan gaba da su, a wani hari da 'yan tawayen kasar Uganda na ADF suka kai garin Beni na gabashin kasar D/Congo a daren jiya Alhamis.

Majiyar ta ce 'yan tawayen na Ugnada sun far wa wata Mota a mashigar garin na Beni tare da yin awan gaba da mutanan dake cikin ta.

A nasu bangare, magabatan garin Beni sun bukaci a gaggauta sakin wadanda aka yi garkuwar da su, tare da gargadin gwamnati game da yiyuwar kai farmaki na 'yan tawayen Uganda  daga arewa zuwa kudancin kasar.

Tun daga shekarar 1994 ne 'yan tawayen na Uganda suka fara kai hare-hare a gabashin kasar D/Congo,inda suka kashe dariruwan mutane a yankin Beni dake jahar Kivo ta arewa dake gabashin kasar ta Congo.

Hukumomin kasar Congo da tawagar wakilan MDD a kasar sun sanar da cewa daga watan Oktoban 2014 zuwa yanzu 'yan tawayen na Uganda sun kashe fararen hula sama da 700 a wannan yanki.

Jan 12, 2018 19:10 UTC
Ra'ayi