• Dubban Yan Kasar Kongo Sun Yi Gudun Hijira Zuwa Burundi

Yan sanda a kasar Burundi sun bada labarin shigowar dubban yan kasar Demokradiyyar Kongo cikin kasar sanadiyar yaki tsakanin yan tawaye da sojojin a kasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto majiyar yan sandan tana cewa a cikin kwanaki uku da suka gabata yan gudun hijira daga yankin Kivu ta kudu kimanin dubu 7 ne suka shiga gabacin kasar Ruwanda.

Amma jami'an hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar dinkin duniya da suke kasar har yanzun ba su bada wata sanarwa dangane da hakan ba. 

Kafin haka dai shugaban kasar ta Demokradiyyar Kongo ya bayyana cewa ana fama da tashe-tashen hankula a yankunan Kivu ta kudu da kuma ta Arewa a cikin yan kwanakin nan. 

Tags

Jan 27, 2018 11:52 UTC
Ra'ayi