Jan 30, 2018 12:13 UTC
  • Ana Ci Gaba Da Yin Kira Kan A Kaurace Wa Zaben Shugaban Kasa A Masar

Masu rajin kare hakkin bil'adama da kuma yan siyasa a kasar Masar suna ci gaba da kiran mutanen kasar su kaurace wa shiga zaben shugaban kasa mai zuwa.

Shafin yanar gizo na Arabi-21 ya nakalto wani bayani wanda wadannan mutane suka rattabawa hannu, wanda ya ce zaben shugaban kasa mai zuwa a kasar ya rasa mafi karancin abin da zai halatta shi, ba don komai ba sai don shishigin da jami'an tsaro suke yi a cikin lamurran siyasar kasar.

Bayanin ya bukaci mutanen kasar Masar kada su amince da zaben kuma ko an gudanar da shi kada su amince da sakamakonsa. 

Banda haka ma wadanda suka sanyawa wannan bayanin hannu sun bayyana cewa zaben kasar mai zuwa sharar fage ne na gabatar da sauye-sauyen a cikin kundin tsarin mulkin kasar wanda zai bawa shugaba Alsisi damar shugabancin kasar har illamasha'allah. 

Da alamun za'a gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Masar a wannan shekara, inda shugaban kasa mai ci Abdul Fatah Al-sisi ne kadai dan takarar shugaban kasa a cikinsa.

Tags

Ra'ayi