Feb 06, 2018 05:39 UTC
  • An Cimma Yarjejeniyar Tsaro Tsakanin Kasashen Sudan Da Sudan Ta Kudu

Kwamitin hadin gwiwa na tsaro tsakanin kasashen Sudan da sudan ta kudu ya kamala taronsa bisa shiga tsakanin kungiyar tarayar Afirka a birnin Addis Ababa na kasar Ethiopia.

Tashar talabijin din Aljazeera ta nakalto Kuol Manyang ministan tsaron kasar sudan ta kudu da Emad Din Adawi shugaban rundunar hadin gwiwa na kasar Sudan a daren lahadin da ta gaba sun sanya hannu kan yarjejeniyar da suka cimma a bangaren tsaro bisa sanya idon wakilin kungiyar tarayar Afirka Tabo Mikey tsohon shugaban kasar Afirka ta kudu.

A yayin zaman kwamitin, bangarorin biyu sun cimma matsaya kan zartar da yarjejeniyar da suka cimma na aiki tare tsakanin kasashen biyu da kuma magance sabanin dake tsakaninsu na ballewar kasar Sudan ta kudu daga kasar ta Sudan.

Bayan shekaru biyu kacal da Sudan ta kudu ta balle daga kasar Sudan din a shekarar shekarar 2011, kasar ta fada cikin yakin basasa, bayan da shugaban Salva Kiir ya sauke mataimakinsa Riek Machar daga kan mukaminsa.

Tags

Ra'ayi