• A Jiya Laraba Ne Aka Gudanar Da Jana'izar Sheikh Qasim Umar Sokoto

A jiya ne aka gudanar da jana'izar Malam Kasimu Umar wakilin 'yan uwa musulmi (Harkar Musulunci) a Sokoto, wanda ya rasu bayan fama da jinya sakamakon harbin da 'yan sanda suka yi masa a wata muzaharar neman sakin shugaban Harka Islamiya a kasar sheikh Ibrahim El Zakzaky.

Sheikh Kasimu Umar  daya daga cikin shuwagabannin Harka Islamiya karkashin shugabancin Sheikh Ibrahim Zakzaky an yi jana'izarsa ne a jiya Laraba a garin Sokoto, bayan ya yi ta fama da jinya saboda albarusan da suka same shi a jerin gwano a Abuja kimanin makonni biyu da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran hukumar radio da talabijin na Iran ya nakalto cewa, Sheikh Qasim Sokoto yana sahun gaba a zanga-zangar neman a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky makonni biyu da suka wuce a birnin Abuja babban birnin Kasar, inda a nan ne wasu albarusan jami'an tsaro suka same shi. Sannan bayan jinya na makonni biyu ya rasu a ranar Litinin.

Magoya bayan Sheikh Ibrahim Zakzaky sun kara kaimi wajen ci gaba da gudanar da zanga-zangar da suke yi domin ganin an sake shi, domin sama masa magani sakamakon yadda yanayin lafiyarsa ke ci gaba da tabarbarewa a inda ake tsare da shi.

Tags

Feb 08, 2018 06:48 UTC
Ra'ayi