• Sojojin Najeriya Sun Fara Wani Shiri Na Musamman Don Dawo Da Tsaro A Jihohi 6 Na Kasar

Rundunar sojin Najerya ta fara jigilar sojoji zuwa jihohi 6 na kasar don yaki da matsalolin tsaro, matsalolin da suka hada da rikicin makiyaya da manoma, sata da garkuwa da mutane, satar shanu da kuma fashi da makami.

Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta nakalto babban kwamandan sojojin kasar Laftanar janar Tukur Buratai yana fadar haka a jiya Laraba, ya kuma kara da cewa wannan gagarumin aikin zai soma daga yau Alhamis, kuma zai hada da jihohin Benue, Taraba, Kogi, Nasarawa, Kaduna da kuma Niger.

Burutai ya ce rundunar sojojin Nigeria ta bawa wannan gagarumin aiki suna "Tseren Mage" kuma sojojin nasu zasu dauki makonni 6 cur suna aiwatar da shirin. 

Tukur Buratai ya ce wannan shirin na sojojin kasar wani tallafi ne ga sauran jami'an tsaron kasar . Manja David Ahmadu shugaban bangaren horaswa na rundunar wanda kuma yake magana da yawun Tukur Buratai ya ce tuni rundunar ta sanar da gwamnonin jihohin da abin ya shafa, kuma sauran jami'an tsaron kasar zasu yi aiki tare da rundunar sojojin kasar kafada da kafada.

 

Tags

Feb 08, 2018 06:49 UTC
Ra'ayi