• Sudan Ta Kore Cewa Turkiya Na Shirin Gina Sansanin Soja A Tsibirin Sawakin

Ministan harkokin wajen Sudan Ibrahim Gandur ne ya kore haka a yayin taron manema labaru da takwaransa na Masar Samih Shukri

Ministan harkokin wajen kasar ta Sudan ya kara da cewa; Tsibirin Sawakin mallakin Sudan, don haka 'yan Sudan ne kadai za su kasance a cikinsa.

Bugu da kari Ibrahim Gandur ya ce; ko kadan ba su tattauna batun gina sansanin soja da Turkiya ba.

Har ila yau ministan harkokin wajen Sudan ya ce; Shugaban kasar Turkiya ya ba da shawarar sake gida tsofaffin gidajen da suke a tsibirin ne da mayar da yankin zama wurin yawon bude ido.

Tsibirin na Sawakin ya kasance daya daga cikin cibiyoyin kasuwanci a lokacin daular Usmaniyya ta Turkiya.

A ziyarar karshe da shugaban kasar Turkiya  Rajab Tayyib Urdugan  ya kai zuwa kasar Sudan, kasashen biyu sun kulla yarjejeniya akan bunkasa tsibirin.

Tags

Feb 09, 2018 11:55 UTC
Ra'ayi