Feb 09, 2018 14:19 UTC
  • Masar Ta Kaddamar Da Samamen Murkushe 'Yan Ta'adda

Rundinar Sojin Masar ta kaddamar a yau Juma'a da wani katsaitacen samame mai manufar yaki da ta'addanci a duk fadin kasar, ciki har da yankin Sinai da ya jima yana fama da matsalar mayakan jihadi.

Kakakin rundinar sojin kasar, Tamer el-Refai, ya fada a wani jawabi a gidan talabijin din kasar cewa : shirin na da manufar kawar da duk wata barazanar ta'addanci da kuma masu aikata muggan laifi.

Shirin dai ya tanadi karfafa bincike a iyakoki domin tsarkake yankunan daga 'yan ta'adda. 

Tini dai sojojin da 'yan sanda kasar suka sanar da shiga shirin ko ta kwana mafi girma a wadanan yankunan.

Tun dai bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin Mohamed Morsi a 2013, dakarun kasar ke ci gaba da fafatawa da 'yan tada kayar baya ciki har da na reshen kungiyar 'yan ta'adda ta IS a yankin Sinai dake arewa maso gabashin kasar. 

Alkalumma sun nuna cewa tun lokacin daruruwan 'yan sanda da sojojin Masar ne suka hallaka a galibin farmaki da hare haren da kungiyar IS ke daukar alhakin kaiwa.

Tags

Ra'ayi