• Libiya : An Kai Hari A Wani Masallacin Benghazi

A Libiya a kalla mutum guda ne ya rasa ransa kana wasu 62 na daban suka jikkata a wani hari da aka kai a wani masallaci dake Benghazi birnin na biyu mafi girma a kasar.

Majiyoyin asibiti sun shaidawa masu aiko da rahotanni cewa da akwai masu munanen raunuka a cikin wadanda lamarin ya rusa dasu.

Bayanai daga kasar sun ce bama bamai biyu ne suka fashe a lokacin da ake sallar Juma'a a masallacin Saad Ibn Abou Abada dake tsakiyar birnin na Benghazi.

Wata majiyar tsaro ta shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa an sanya bam guda a cikin akwatin daukar gawa dake cikin masallacin, a yayin na biyu aka dana shi a wurin ajiye takalmi a mashigar masallacin.

Har zuwa lokacin fasara wadanan labaren babu wata kungiya data dau alkahin kai harin.

Wannan dai ba shi ne karo farko ba da ake fuskantar irin wannan hari ba a Benghazi, don ko a ranar 23 ga watan Janairu wani makamancinsa ya yi ajalin mutum 40.

Tags

Feb 09, 2018 16:34 UTC
Ra'ayi