• Nijar Ba Ta Bawa Talakawa Haske A Kasafin Kudi _ Rahoto

Kungiyar kare hakkin bil adama ta (Alternative Espace Citoyens) ta fitar da wani rahoto da ya ambato Jamhuriya Nijar a cikin jerin kasashen da ba sa bayar da haske a kasafin kudin da suka tanada wa talakawan su.

Binciken wanda kungiyar ke gudanarwa a cikin shekaru biyu-biyu a fadin duniya ya nuna cewa Nijar bata samu baki ko guda ba cikin dari.

Sau biyar ana gudanar da irin wannan bincike a Nijar, inda a shekara 2008 kasar ta samu maki 26 cikin 100, saidai wannan karo bata samu maki ko guda ba.

Wasu kungiyoyin fara hula a kasar sun ce rahoton bai zo masu da mamaki ba, saboda hukumomin kasar basu ciki yin haske ba a kasafin kudin, sannan basu cika wallafa shi ba a yanar gizo.

Rahoton ya ce baya ga Nijar akwai kasashen da suka hada da : Yemen, Qatar, Lesoto da Equatorial Guinea da Venezuella wandanda basu samu maki ko guda ba.

Tags

Feb 09, 2018 18:09 UTC
Ra'ayi