• Buhari Ya Jagoranci Taron Majalisar Tsaron Kasa Kan Yanayin Tsaro A Nijeriya

Sakamakon ci gaba da matsaloli na tsaro da ake fuskanta a Nijeriya, shugaban kasar Muhammadu Buhari ya jagoranci wani zama na majalisar tsaron kasar a fadarsa da ke Abuja don tattauna batutuwan tsaron da kuka daukar matakan da suka dace wajen magance su.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN ya bayyana cewar taron na yau dai wanda aka fara gudanar da shi da rana ya sami halartar dukkanin hafsoshin sojin kasar, sufeto janar na 'yan sanda, shugabannin cibiyoyin tsaro na kasar, wasu ministoci da dai sauran jami'an da abin ya shafa karkashin jagorancin shugaban kasar Muhammadu Buhari.

A wani sakon da ya fitar a shafinsa na Twitter, shugaba Buharin ya ce a yau din ya jagoranci taron majalisar tsaron bisa la'akari da matsalolin tsaron da ake fuskanta, yana mai cewa a shirye suke su dau matakan da suka dace wajen magance matsalolin tsaron da ake fuskanta.

Duk da cewa ba a yi karin bayani kan hakikanin batutuwan da aka tattauna din ba, to sai wasu majiyoyi suna nuni da cewa daga cikin batutuwan da ake tunanin an tattauna a yayin zaman har da batun matsalar Boko Haram da kuma sako wasu malaman jami'a guda uku da wasu 'yan sanda mata da kungiyar ta sako su kwanakin baya bayan sacewa su da suka yi.

A ranar Asabar din da ta gabata ce dai hukumar tsaro kasa ta SSS ta yi wa shugaba Buharin karin bayani dangane da tattaunawar da ake yi da kungiyar Boko Haram din don sako wadannan mutanen.

 

Tags

Feb 12, 2018 17:57 UTC
Ra'ayi