Feb 13, 2018 06:35 UTC
  • Afirka Ta Kudu: ANC Ta Bayar Da Wa'adin Sa'oi 48 Ga Zuma Da Ya Yi Murabus

Jam'iyyar ANC mai mulki a kasar Afirka ta kudu ta bayar da wa'adin kwanaki biyu ga shugaba Jacob Zuma da ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban kasar, ko kuma a tsige shi.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, a zaman da manyan kusoshin jam'iyyar ANC mai mulki a Afirka ta kudu suka gudanar na tsawon sa'oi 8 a jere, sun bukaci shugaba Jacob Zuma da ya sauka daga kan mukaminsa, ko kuma a kada kuri'ar tsige shi a majalisar dokoki, inda jam'iyyar take da rinjaye.

Wasu majiyoyi a cikin jam'iyyar ta ANC sun ce, mataimakin shugaban kasar kuma shugaban jam'iyyar ta ANC Cyril Ramaphosa, shi ne  da kansa ya nufi fadar shugaban kasar da ke Pretoria, domin sheda wa shugaba Zuma matsayar da jam'iyyar ta yanke.

Kafofin yada labaran Afirka ta kudu dai sun ce Zuma ya amince ya sauka, amma bisa amincewa da wasu sharudda da ya gindaya.

Tags

Ra'ayi