Feb 13, 2018 15:34 UTC
  • Nijar : Isufu, Ya Aike Wa Takwaransa Na Iran Sakon Taya Murna

Shugaba Isufu Mahamadu, na Jamhuriya Nijar , ya aike wa da takwaransa na Iran, Dakta Hassan Ruhani, sakon taya murna dangane da zagayowar shekaru 39 da nasara juyin juya halin musulinci a Iran.

A cikin sakonsa, Alhaji Isufu Mahamadu, ya yaba da dakon zumunci da hadadiyar alaka dake tsakanin kasashen biyu da al'umominsu, wanda ya ce babban ci gaba ne a tsakanin gwamnatocin biyu.

Shugaba Isufu, ya kuma kara jadadda wa takwaransa na Jamhuriya musulinci ta Iran aniyarsa ta ci gaba da yin aiki tare, domin kara karfafa alakar dake tsakanin kasashen biyu.

A ranar Lahadi da ta gabata ne 11 ga watan Fabrairu, Iran ta yi bikin cika shekaru 39 da samun nasara juyin juya halin musulinci a kasar, karkashin jagorancin mirigayi Imam Khomaini.

Juyin juya halin musuluncin a Iran wanda ya cika shekaru 39 da samuwarsa, ya kawo sauyi sosai a kasar da ma yankin.

Tags

Ra'ayi