• Afrika Ta Kudu : Zuma Zai Bayyana Matsayinsa Ranar Laraba

Wasu majiyoyi daga AFrika ta Kudu na cewa, shugaban kasar Jacob Zuma dake fusknatr matsin lamba zai bayyana matsayinsa a gobe Laraba.

Jam'iyyar ANC mai mulki a kasar dai ta bukaci Mista Zuma, da ya yi murabus a hukumance ko kuma ta yi masa kiranye.

Kafin nan dai wani jami'i ya bayyana cewa, Shugaba Zuma ya shaida musu zai yi murabus amma nan da wata uku zuwa shida.

Shugaba Zuma dai ya ce yana bukatar ya halarci taron shugabannin Kasashe masu samun habakar tattalin arziki da ake kira BRICS wanda kasarsa za ta karba a cikin watanni masu zuwa a birnin Johannesburg, saidai akayi watsi da wannan bukata tasa.

Wani jigo a jam'iyyar ta (ANC), Ace Magashule, ya bayyana cewa, jam'iyyar na son Mista Zuma ya ya murabus ba da bata lokaci ba, saboda ci gaban kasar, kuma ci gaba da kasancewar a wannan mukami zai sa jam'iyyar ta sha kashi a zabe mai zuwa.

Tun a watan Disamba ake matsa wa Mista Zuma, wanda ya hau mulkin kasar tun 2009, lamba akan ya yi murabus kan zarge-zargen cin hanci.

Tags

Feb 13, 2018 16:25 UTC
Ra'ayi