Feb 14, 2018 05:57 UTC
  • Wa'adin Sa'oi 48 Ga Shugaba Zuma Da Ya Sauka Daga Karagar Mulkin Afirka Ta Kudu

A ci gaba da rikicin siyasa da ya kunno kai a kasar Afirka ta Kudu, jam'iyyar ANC mai mulki a kasar, a wani zama da ta gudanar a jiya Talata karkashin jagorancin shugabanta Cyril Ramaphosa, ta ba wa shugaban kasar Jacob Zuma wa'adin sa'oi 48 da yayi murabus daga karagar mulki ko kuma a fara shirin tsige shi.

Shugaba Zuma din dai wanda ya dare karagar mulki a shekara ta 2009 yana fuskantar tuhumce-tuhumce na rashawa da cin hanci ne, wanda a sannu a hankali lamarin ya ci gaba da girmar da ya kai a halin yanzu hatta 'yan jam'iyyarsa da tsoffin abokansa su ne kan gaba wajen kiransa da yayi murabus duk kuwa da ci gaba da musanta wannan zargi da yake yi.

Wadannan tuhumce-tuhumce dai su ne suka sanya a lokutan baya masu adawa da shi sun yi ta kokarin tilasta masa yin murabus. Daya daga cikin irin wadannan kokarin shi ne kudurin da 'yan adawan suka gabatar a majalisar kasar a shekarar bara don kada kuri'ar tsige shi, lamarin da bai yi nasara ba. Don da cewa a halin yanzu ma a ranar 22 ga wannan watan da muke ciki na Fabrairu, 'yan adawan za su sake gwada sa'a a kuri'ar tsige shi din da za a kada. Tsawon wannan lokacin dai shugaba Zuman yayi kokari wajen rage irin wannan matsin lambar da ake masa da kuma neman yardar masu adawa da shi din ta hanyar yin garanbawul ga gwamnatinsa da sallamar wasu ministocin, to sai dai daga dukkan alamu hakan ba ta haifar masa da da mai ido ba.

Ci gaba da tabarbarewar yanayin tattalin arziki da karuwar fatara da rashin aikin yi a kasar Afirka ta Kudun na daga cikin lamurran da suke kara matsin lambar da shugaba Zuman yake fuskanta da kuma kara dushe irin kaunar da al'umma suke masa. Hakan ne ya sanya manyan jami'an jam'iyyar ANC mai mulki wacce kuma ta kasance jam'iyya mafi girma da jama'a a kasar sakamakon irin gwagwarmaya da wariyar launin fata da ta yi a kasar, shiga cikin damuwar cewa ci gaba da mulkin Jacob Zuman na iya haifar mata da matsala da kuma rage mata yawan magoya bayan da take da su.

Hakan ne ma ya sanya a zaben cikin gida da aka gudanar a watan Disambar bara, 'yan jam'iyyar suka zabi Cyril Ramaphosa,  wanda shi ne mataimakin shugaba Zuman, a matsayin shugaban jam'iyyar ANC din don maye gurbin shugaba Zuman a wannan matsayin. A halin yanzu dai Mr. Ramaphosan shi ne kan gaba wajen yin matsin lamba wa shugaba Zuman da ya sauka daga karagar mulkin lamarin da zai ba shi damar darewa karagar mulkin alal akalla har zuwa shekara mai zuwa lokacin da za a gudanar da zaben shugaban kasar.

A wani lokaci a yau ne dai ake sa ran shugaba Zuman, a wata ganawa da manema labarai da zai yi, zai fadi matsayarsa kan wannan kirayen da jam'iyyar ANC din ta yi da kuma wa'adin da ta ba shi na yin murabus din. Wasu majiyoyin suna nuni da cewa shugaba Zuma ya amince da yin murabus din amma bisa wasu sharudda.

Masana al'amurran yau da kullum dai suna ganin a irin wannan yanayin shugaba Zuman ba shi da wata mafita face dai ya amince da bukatar jam'iyyar tasa, don kuwa kin amincewa da hakan na iya kai wa ga tsige shi a majalisa, wanda hakan kuwa ba zai yi masa kyau da kuma ita kanta jam'iyyar ba don hakan zai kara rarraba kan 'yan jam'iyyar ne.

Tags

Ra'ayi