Feb 14, 2018 06:15 UTC
  • Daliban Makaranta Kimani 22 Suka Rasa Rayukansu A Wani Hatsarin Muta A Kano

Daliban makarantar sekandari ta Masau a jihar Bauchi 22 suka rasa rayukansu a lokacinda motar bus da take dauke dasu ta yi karon gaba da gaba da wata Daf a kan hanyarsu ta zuwa Kano a garin gaya.

Kamfanin watsa labarai na muryar jumhuriyar musulunci ta Iran ya nakalto daga jaridar Daily Trust wacce ta nakalto Jami'an watsa labarai na hukumar kula da hatsarurruka ta kasa  Road Safety Corps (FRSC) ta Kano Kabiru Ibrahim Daura yana tabbatar da labarin.

Jami'in ya kara da cewa hatsarin ya auku ne da misalin karfe 11 na safe, a garin Tsaida na karamar hukumar Gaya. Ibrahim ya kara da cewa 12 daga cikin daliban da suka rasa rayukansu maza ne a yayinsa 10 kuma mata ne. Sannan sannan wasu ukku da suka tsira da raunuka suna jinya a gaya da kuma Kano.

Daura ya ce an kai sauran gawakin zuwa babban asbitin Gaya. 

 

Tags

Ra'ayi