Feb 21, 2018 17:38 UTC
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Aike Da Taimako Ga 'Yan Gudun Hijira A Sudan Ta Kadu

Majiyoyin majalisar dinkin duniya sun sanar da aikewa da taimako ga mutane fiye da miliyan biyar da suke bukatar dauki a kasar Sudan ta kudu.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa, an fara bayar da wannan taimako ne tun daga shekarar da ta gabata, kuma ya zuwa yanzu kimanin mutane miliyan 5.4 suka samu taimakon.

Bayanin ya kara da cewa, sakamakon matsalolin da kasar Sudan ta kudu ta fuskanta na yakin basasa, da kuma matsalar fari a mafi yawan yankunan kasar, wannan ya sanya adadin masu bukatar taimako ya karu matuka, inda yanzu mutane miliyan 7 ne suke bukatar taimakon majalisar dinkin duniya da na kungoyin bayar da agaji na kasa da kasa.

Adadin mutanen mutane da suka fice daga kasar suka shiga kasashe makwafta ya kai miliyan uku, wadanda aka tsugunnar da su a sansanonin majalisar dinkin duniya.

Tags

Ra'ayi