Feb 23, 2018 15:37 UTC
  • Sudan Ta Kudu : An Yanke Wa Wani Tsohon Kanal Na Afrika Ta Kudu Hukuncin Kisa

Wata kotu a Sudan ta Kudu ta yanke hukuncin kisa ga wani tsohon kanal na sojin Afrika ta Kudu, bisa tuhumarsa da yunkurin kifar da gwamnati.

Tsohon Kanal din, William John Endley, wanda tsohon mashawarcin jagoran 'yan tawaye na kasarne Riek Mashar, kotun ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya, bisa yunkurin neman kifar da halatacciyar gwamnatin da leken asiri a cewar alkalin kotun ta Juba, Lado Eriminio. 

Kotun ta ce wanda ake tuhumar, zai sha dauri na shekara tara da watanni hudu kafin lokacin da ake sa ran a zartar masa da hukuncin kisan, duk da cewa yana da damar daukaka kara.

Lauyen tsohon kanal din, Gar Adel, ya ce, wannan hukuncin bai zo masu da mamaki ba, kasancewar tun tashin farko kotun ta nuna son rai a cikin shari'ar.

A watan Agusta na 2016 ne aka cafke tsohon kanal din a filin jirgin saman Juba, makwanni kadan bayan kazamin fadan da aka gwabza a babban birnin kasar tsakanin dakarun dake biyaya ga shugaban kasar Salva Kiir da jagoran 'yan tawayen kasar Riek Machar. 

Tags

Ra'ayi