Feb 26, 2018 19:09 UTC
  • Sudan Ta Kudu Na Fama Da Fari

Majalisar Dinkin Duniyar ce ta sanar da bullar fari a cikin sassa daban-daban na kasar Sudan Ta Kudun.

Kamfanin dillancin labarun Associated Press ya nakalo wani sabon rahoton da Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar akan Sudan Ta Kudu wanda yake ishara cewa da akwai mutane miliyan shida a kasar da suke fuskantar hatsari saboda farin.

Rahoton ya kuma ce a shekarar bana an sami karuwar adadin wadanda farin zai rutsa da su da kawo 40% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Wani sashe na rahoton ya ce; Daga lokacin da aka fara yaki a kasar a 2013 zuwa yanzu kaso 1/3 na al'ummar kasar sun bar gidajensu zuwa wasu yankuna, lamarin da ya taimaka wajen samun koma-baya a harkar noma da abinci.

 

Tags

Ra'ayi