Feb 27, 2018 09:59 UTC
  • Afrika Ta Kudu : Ramaphosa, Ya Nada Sabuwar Gwamnati

Sabon shugaban Afrika, Cyril Ramaphosa, ya kafa sabuwar majalisar ministocinsa mai mambobi kimanin talatin.

Mista Ramaphosa, ya kuma mika mukamin mataimakin shugaban kasa ga David Mabuza, babban jigo na biyu a Jam'iyyar ANC.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan murabus din tsohon shugaban kasar, Jacob Zuma, bisa matsin lambar jam'iyyar ANC mai mulki.

Daga cikin wandanda aka nada har da wasu jigan-jigan siyasar AFrika ta Kudun, da tsohon shugaban Zuma ya kora, wanda suka hada da Nhlanhla Nene da aka baiwa ministan kudi da kuma Pravin Gordhan wanda aka nada ministan kamfanonin kasa.

Tags

Ra'ayi