• Ana Gudanar Da Zabe A Kasar Saliyo

A wannan laraba ce, al'ummar kasar Saliyo ke kada kuri'u na zaben sabon shugaban kasa tsakanin 'yan takara 16 bayan da wa'adin shugaban kasar mai ci Ernest Bai Koroma ya kawo karshe.

Sama da mutane milyan 3 ne suka yi rajista domin kada kuri’a a zaben, in da ‘yan takara 16 za su fafata da juna a wannan karamar kasa da ke yammacin Afrika.

Wasu daga cikin ‘yan takarar da suka fi daukar hankulan jama’a a zaben sun hada da Samura Kamara, wanda ya fito daga jam’iyya mai mulki wato APC, sai kuma babban mai hamayya da shi wato Kandeh Yumkella, wanda tsohon mataimakin babban magatakarda na Majalisar Dinkin Duniya da kuma Julius Maada Bio, wanda ya mulki kasar kafin juyin mulki a 1996.

Batun yaki da talauci da kuma samar wa matasa ayyukan yi, su ne suka mamaye yakin neman zaben, lura da cewa a daidai lokacin da Saliyo ke farfadowa daga matsalolin yakin basasa na tsawon shekaru, sai kasar ta sake cin karo da wani ibtila'in  cutar Ebola.

Tags

Mar 07, 2018 11:48 UTC
Ra'ayi