• Kasar Guinee Ta Bukaci Kasashen Tchadi, Da Malesiya Hadewa Da Kungiyar OPEC

Ministan makamashi da ma'adinai na kasar Guinee Equatorial ya bayyana shirin kasashen Kwango, da Tchadi da Malesiya na hadewa da kungiyar kasashe masu arzikin man fetir(OPEC) a takaice

A yayin da yake jawabi na bayan fagen taron Ceraweek da ya gudana a garin Houston na jihar Texas dake kasar Amurka, Gabriel Ambaga Obeyung Ministan makamashi da ma'adinai na kasar Guinee Equatorial ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba kasashen Congo da Tchadi za su kasance cikin kasashen dake fitar da man fetir zuwa kasuwanin duniya.

Mista Gabriel ya tabbatar da cewa akwai wasu kasashen a nahiyar Asiya kamar su Indonosiya dake son komawa cikin kungiyar OPEC, bukatar da kasar Malesiya ta gabatar na hadewa da kungiyar ta OPEC na kan tebirin tattaunawa.

Daga karshe, ministan ya bayyana goyon bayansa kan shawarar da kasar Venezuela ta gabatar na jadadda aikin tawagar kungiyar dake sanya ido kan kasuwar sayar da man fetir din har zuwa shekaru biyar masu zuwa.

Tags

Mar 07, 2018 11:50 UTC
Ra'ayi