• Burundi Ta Mayar da Martani Ga Kwamitin Kare Hakkin Bil Adama Na MDD

Shugaban kwamitin kare hakkin bil adama na kasar Burundi Jean Baptiste Baribonezeka ya mayar da martani ga kwamitin kare hakkin bil adama na MDD, dangane da zargin kisan kiyashi a kasar ta Burundi.

Jean Baptiste Baribonezeka ya sanar da hakan ne a cikin wani bayani da ya fitar, wanda kafofin yada labarai na ciki da wajen kasar suka watsa, inda ya bayyana rahoton baya-bayan nan na kwamitin kare hakkin bil adama na MDD da cewa ya dogara nea  kan bayanai da aka kirkira.

Ya ce kwamitin kare hakkin bil adama ya fitar da bayani kan cewa an yi kisan kiyashi Burundi, ba tare da gabatar da wata kwakwarar hujja kan hakan ba, ya ce bai kamata muhimmin wuri irin wannan ya zama wajen aiwatar da siyasar wasu kasashe a kan wasu kasashen ba.

Dangane da batun kayyade wa'adin shugabanci a kasar Burundi kuwa, Jean Baptiste Baribonezeka ya ce wannan ba aikin kwamitin kare hakkin bil adama na MDD ba ne, hakin kotun kundin tsarin mulkin kasar Burundi ne.

Tags

Mar 07, 2018 17:20 UTC
Ra'ayi