• Kasar Masar Ta Yi Watsi Da Zargin Da Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Kanta

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Masar ta yi kakkausar suka kan Kwamitin Kolin Kula da Kare Hakkin Bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya dangane da rahoton da ya fitar kan kasarta.

A bayanin da ma'aikatar harkokin wajen kasar Masar ta fitar ta yi Allah wadai da sukar da shugaban Kwamitin Kolin Kula da Kare Hakkin Bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya Zaid bin Ra'ad Alhusaini ya yi kan kasar ta Masar tare da zarginta da daukan matakin barazana da tsoratarwa kan 'yan siyasar Masar.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Masar ta kara da cewa: Rahoton Kwamitin Kolin Kula da Kare Hakkin Bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya bai yi la'akari da irin yadda mahukuntan Masar suke kokari a fagen kare hakkin bil-Adama ba, amma sai ya dauki matakin wallafa wasu zarge-zarge marassa tushe da basu da madogara kan kasar.

A ranakun 26 zuwa 28 na wannan wata na Maris ne za a gudanar da zaben shugaban kasa a Masar, inda ake zargin mahukuntan kasar da cusa tsoro a zukatan 'yan siyasa da ake ganin zasu zame barazana ga shugaban kasar Abdul-Fatah Al-Sisi da ke son yin tazarce a wa'adin mulkinsa na biyu. 

  

Tags

Mar 08, 2018 19:01 UTC
Ra'ayi